Dakatar da bada tallafi ga Ruwanda | Labarai | DW | 30.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakatar da bada tallafi ga Ruwanda

Burtaniya ta ce za ta dakatar da bada agajin da ta ke ba Ruwanda bayan da rahotanni su ka nana cewar mahukuntan na Ruwanda na da alaƙa da 'yan tawayen M23 na Kongo.

Rwanda president at int'l aid forum Rwanda President Paul Kagame speaks at the opening ceremony of the 4th High Level Forum on Aid Effectiveness at a convention center in South Korea's largest port city of Busan on Nov. 30, 2011. Some 3,500 representatives from 160 countries are attending the international forum on development assistance. (Yonhap)/2011-11-30 13:45:34/ Keine Weitergabe an Drittverwerter.

Ruandas Präsident Paul Kagame

Sakatariyar cigaban ƙasa da ƙasa ta Burtaniya Justine Greening ce ta ambata hakan inda ta ƙara da cewar a wannan karon ko kusa London ba za ta aikewa da mahukuntan Kigali fam miliyan 21 da ta saba aike mata ba saboda alaƙarsu da M23 domin a cewar Uwargida Gereenings ɗin wani mataki ne na saɓa alƙawarin da ƙasashen biyu su ka yi.

Wannan matsayi da London ɗin ta ɗauka dai wani yunƙuri ne na matsawa Ruwanda lamba da ta tashi tsaye wajen kashe wutar rikicin na Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo to sai dai Ruwandan ta sha musanta wannan zargi da ake mata na agazawa 'yan tawayen.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Usman Shehu Usman