Dakarun Ukraine sun shaida janye makamai daga fagen fama | Labarai | DW | 06.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Ukraine sun shaida janye makamai daga fagen fama

Dakarun gwamnatin Ukraine sun ce su ana janye manyan rokoki daga filin daga tare da bangaren 'yan aware magoya bayan Rasha.

Dakarun gwamnatin Ukraine sun ce su ana janye manyan rokoki daga filin daga tare da bangaren 'yan awaren Rasha.

Mayakan na Ukraine sun ce an yi hakan ne bisa la'akari da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a watan jiya kan rikicin Ukraine din da kuma Rasha.

Wani kakakin sojin gwamnatin Ukraine din Col. Andriy Lysenko, ya shaidawa kamfanin labaran Associated Press cewa, yanzu an janye makamakan ne da kalla kilomita 35 daga bakin dagan.