1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun RSF sun kashe kananan yara a Sudan

December 6, 2025

Wani harin jirgi maras matuki da sojojin sa kai na RSF a sudan suka kai kan wata makarantar yara kanana, ya yi sanadin mutuwar mutane 50 ciki har da yara 33.

https://p.dw.com/p/54t51
'Yan Sudan da ke guje wa yankunan da ake gwabza rikici
'Yan Sudan da ke guje wa yankunan da ake gwabza rikiciHoto: AFP/Getty Images

Ana ganin cewa ta yiwu alkalumman wadanda suka mutu a harin na jihar Kordofan ya karu, sai dai rashin hanyoyin sadarwa a yankin ya haifar da tsaikon ba da rahoton. A cewar wakilin Asusun Kula da Kanana Yara na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan, Sheldon Yett, kashe yara kanana a markatanta babban laifi ne na take hakkin yara.

Ya kara da cewa, bai kamata a ce yara ne ke shan ukubar sakamakon rikicin ba. UNICEF ta bukaci dukannin bangarorin su mayar da wukakensu cikin kube nan take. Daruruwan fararen hula ne aka kashe a Kordofan a makwannin baya-bayan nan, yayin da fada ya koma yankin daga Darfur, bayan da mayakan RSF suka karbe iko da birn el- Fasher.