Dakarun kiyaye zaman lafiya sun shata yankin tsaro a arewacin Mali | Labarai | DW | 18.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun kiyaye zaman lafiya sun shata yankin tsaro a arewacin Mali

Dakarun kiyaye zaman lafiya sun dauki matakin shiga tsakanin bangarorin da ke rikici da juna a yankin arewacin kasar Mali

Dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin duniya da ke kasar Mali sun shata yankin tsaro a garin Kidal na arewacin kasar, domin dakile fada tsakanin bangarori masu dauke da makamai, abin da ke barazana ga yarjejeniyar zaman lafiya wadda take tangal-tangal.

Matakin ya biyo bayan kwashe kwanaki uku ana fafata tsakanin kungyiyoyi masu goyon bayan gwamnati da ke dauke da makamai da kuma na 'yan aware duk na Abzinawa. Lamarin ya janyo mutuwar mutane da dama yayin da gobe Laraba ake shirin fara wani zaman sulhu a kasar Jamhuriyar Nijar mai makwabtaka. Yankin tsaron yana da girma na kimanin kilo-mita 20.

Akwai kimanin dakarun kiyaye zaman lafiya 9000 a kasar ta Mali da ke yankin yammacin Afirka, inda kashi 90 cikin 100 na dakarun suke aiki a yankin arewacin kasar. Tuni gwamnatin kasar ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Afirka su gudanar da bincike kan saba yarjejeniyar da aka kulla ta zaman lafiya tsakanin gwamnati da kungiyoyin 'yan aware.