Dakarun Amurka sun wanke kansu daga rataye Sadam | Labarai | DW | 03.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Amurka sun wanke kansu daga rataye Sadam

Dakarun sojin Amurka dake Iraki sun bayyana cewa basu da hannui a zartar da hukuncin Rataye tsohon shugaba Sadam Hussein,domin da sune da ba haka zasu aiwatar da bhukuncin kisan ba.Major General William Caldwell ya fadawa taron manema lamaru cewa,dakarun Amurka basu da hannu da Sadam da rataya da akayi masa,tun bayan da suka mika shi zuwa hannun hukumomin Irakin ,kamar yadda gwamnatin kasar ta bukata.Wannan furuci na Amurkan yazo ne adai dai lokacin da ake cigaba da korafe korafe kann yadda jamian darikar Shian suka tozarta wa Sadam gabannin rataye shi.A halin da ake ciki yanzu kuwa rahotannin wasu kafofin yada labaran kasashen larabawan na nuni dacewa,a gobe ne zaa rataye sauran mutane biyu da aka yankewa hukuncin kisa tare da Sadam,wadanda suka hadar da dan uwansa.