1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin bayan zabe a Cote d'Ivoire

Abdoulaye Mamane Amadou
November 7, 2020

Jami'an tsaron Cote d'Ivoire sun cafke daya daga madugun 'yan adawar kasar Affi N'Guessan kamar yadda majiyar jam'iyyarsa ta Front Populaire Ivoirien (FPI) ta sheda wa manema labarai.

https://p.dw.com/p/3kzSU
Elfenbeinküste Wahl 2020 | PK Pascal Affi N'Guessan FPI
Hoto: Luc Gnago/REUTERS

 

Wata majiya daga gwamnatin kasar ta ce an kama Mista Affi N'Guessan ne da ya jima yana kulli kurciya da 'yan sanda a wani gari kusa da iyakar kasar da Ghana a yayin da yake neman tserewa, lamarin da magoya bayan jam'iyyarsa suka musanta.

A yammacin ranar Alhamis ne babban mai shigar da kara na gwamnati ya zargi jiga-jigan 'yan adawar da laifukan tada zaune tsaye a kasar da suka hada da kisa da aiyukan ta'addanci kana kuma hukuma na nemansa ruwa jallo.

'Yan adawar kasar dai sun bayyana kuracewa shiga zaben shugaban kasar na ranar 31 ga watan jiya, tare da kafa wata gwamnatin rikon kwarya kwanaki bayan da aka bayyana shugaba Alassane Ouattara a matsayin wanda ya yi gagarumin nasara zaben mai cikre da cece-kuce.