1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar kwalara ta kunno kai a Mozambik

Mouhamadou Awal Balarabe
March 28, 2019

Mutane biyar sun kamu da cutar amai da gudawa a wata unguwar marasa galihu da ke kewayen birnin Beira na kasar Mozambik. Hukumomi sun fara kokarin samar da ruwa mai tsafta tare da da tsabtace gari.

https://p.dw.com/p/3FmwO
Mosambik | MSN in Punta Gea
Hoto: MSF/Pablo Garrigos

Hukumomin Mozambik sun tabbatar da bullar cutar kwalara a yankin kasar da ya fuskanci iftila'in mahaukaciyar guguwar Idai gami da ambaliyar ruwa da suka lalata dukiyoyi da salwantar da rayuka. Dama hukumomin kiwon lafiya da kungiyoyin agaji sun yi gargadin cewa ana iya fuskantar barazanar cututtuka sakamakon gurbacewar yanayin rayuwa.


Wadanda suka kamu da cutar kwalara sun kai biyar a Munhava, wata unguwar marasa galihu da ke kewayen birnin Beira. Hukumomi Mozambik na kokarin samar da ruwa mai tsafta tare da da tsabtace gari .Daruruwa ko ma dubban mutane ne suka mutu a wannan iftali'in.

Amma Hukumar Lafiya ta Duniya tana ci gaba da jan hankali kan yiwuwar "bala'i na biyu" na bullar cututtuka idan ba a dauki matakan gaggawa ba. Tuni ma WHO ko OMS ta samar da allurar rigakafi dubu dari tara da za su iso a mako mai zuwa a cikin kasar.