Lafiya
Cutar Ebola ta kashe mutane 17 Kwango
May 8, 2018Talla
Jami'ai a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango sun tabbatar da cewa kimanin mutane 17 suka hallaka sakamakon cutar Ebola da ta bulla a kasar.
Mahukunta sun ce cutar ta bulla cikin yankin arewa maso yammacin kasar. Tun a makon jiya ranar 3 ga wannan wata na Mayu aka samu rahoton bullar cutar inda kimanin mutane 21 suka kamu da zazzabi daga ciki 17 suka rasu. Sakamakon da aka samu a cibiyar bincike da ke birnin Kinshasa ya tabbatar da cewa biyu daga cikin mutanen sun kamu da cutar Ebola.