Cutar Ebola ta hallaka mutane 70 a Guinea | Labarai | DW | 30.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cutar Ebola ta hallaka mutane 70 a Guinea

Ƙasar Senegal ta rufe iyaka da Guinea Conakry domin kariya daga cutar Ebola

Ƙasar Guinea Conakry ta bayyana ɗaukan matakan daƙile cutar zazzabin Ebola da ta hallaka mutane 70 kuma take barazanar yuɗuwa zuwa ƙasashe maƙwabta. Cutar wadda ta fara ɓulla daga yankin kudancin ƙasar yanzu ta yaɗu zuwa sauran sassa. Tuni Ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi alƙawarin bai wa ƙasar Euro milyan 500 domin daƙile cutar ta Ebola, wadda rahotanni ke cewa ta shiga ƙasar Saliyio da wasu sauran ƙasashe maƙobta. Cikin wani matakin rigakafi gwamnatin ƙasar Senegal ta bayyana rufe kan iyakar ƙasar da Guinea Conakry. Wata sanarwa ta ma'aikatar harkokin cikin gidan ƙasar ta Senegal, ta ce kan iyaka da Guinea zai ci gaba da kasancewa a garƙame har zuwa lokacin da gwamnati za ta sake fitar da sanarwa. Mahukuntan ƙasar ta Guinea Conakry sun ce babu tabbacin yadda cutar ta Ebola ta shiga cikin ƙasar da ke yankin yammacin Afirka.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane