CPJ: Aikin jarida na fuskantar barazana | Labarai | DW | 25.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

CPJ: Aikin jarida na fuskantar barazana

A wani rahoto da ta fitar kungiyar kare hakkin yan jarida ta duniya ta ce kafofin yada labarai na fuskantar sabbin barazana na dakile yancin fadin albarakacin baki da kuma tursasawar gwamnatoci.

LOGO CPJ

A rahotonta na shekara shekara wanda aka wallafa a matsayin cikakken littafi da ta yiwa lakabi da hari kan kafofin yada labarai, kungiyar kare hakkin 'yan jarida ta duniya CPJ ta ce gwamnatoci na amfani da dabaru masu sarkakakiya wajen danne harkokin yada labarai da kuma tauye sukar lamirinsu.

Joel Simon shugaban kungiyar yace matakin wanda ke kara yin kamari babban abin damuwa ne matuka, musamman yace batun yada labaran karya da kuma barazana ga yanayin aikin jarida da suka wanzu tun bayan zaben shugaban Amirka Donald Trump.

Kungiyar ta yi nuni da cewa kasashe kamar Rasha da China da kuma Mexico suna sauya alkiblar muhawara a shafukan Internet ta amfani da 'yan baranda masu yada farfaganda, yayin da Amirka kuma ke sa ido tare da goge wasu bayanai da sunan yaki da ta'addanci.