COVID-19 Senegal na yin nasara | Labarai | DW | 12.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

COVID-19 Senegal na yin nasara

Hukumomi a kasar Senegal sun bayar da sanarwar bude masallatai da mujami'u a woni kokarin farfado da harkokin walalar jama'a bayan barkewar annobar coronavirus

Shugaba kasar ta Senegal Macky Sall shi ne ya bayar da wannan sanarwar tare da sassauta dokar hana zirga-zirga da aka kakaba domin yaki da annobar Corona.

Kasar ta Senegal na kan gaba cikin kasashen duniya da suka ci karfin annobar ta coronavirus da ta kama mutane 1886 a kasar, inda tuni 715 suka murmure daga cutar, kana mutune 19 ne  suka mutu bayan kamuwa da cutar.

A wani yunkuri na baya-bayan nan, kasar ta fara gwajin na'urorin gwajin cutar cikin mintoci 10, kuma masu saukin kudi da mutum zai iya gwada kansa daga gida. Haka zalika gwamnatin Senegal ta amince a gwada maganin gargajiya da aka samu a kasar Madagaska.