1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Raba alluran rigakafi masu inganci

Zainab Mohammed Abubakar
December 1, 2021

Shirin tallafin rigakafin corona na Covax ya jaddada bukatar kasashe masu arziki su baiwa matalauta ingantattun allurai ba wadanda aikinsu ya kusan karewa.

https://p.dw.com/p/43iJT
Senegal Coronavirus l Flughafen von Dakar, Covax, Impfdosen
Hoto: John Wessels/AFP/Getty Images

Shirin na Covax wadda hukumar kula da lafiya ta MDD ta kirkira da hadin gwiwar wasu kamfanonin harhada magunguna da allurai, na da nufin tabbatar da cewar rigakafin na corona ya isa ga kasashe marasa galihu 'yan rabbana ka wadatamu.

Shugaban Gavi daya daga cikin kamfanonin hadakar, Seth Berkley  ya wallafa a shafinsa na twitter cewar, cikin sao'i 24 kacal an aike da alluran rigakafin wajen miliyan 11 zuwa kasashe shida.

Shirin na Covax yayi fatan raba allurai wajen biliyan biyu cikin wannan shekara ta 2021 mai karewa, sai dai kawo yanzu milyan 563 kawai aka cimma rabawa.

Ana zargin kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya da nuna banbanci wajen rabon rigakafin, wanda ya bada damar bayyanar wasu nauuo'i na cutar kamar Omicron da ke da asali daga Afirka ta Kudu.