1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane kusan 3,200 ake san zasu fice daga Cote d'ivore

November 3, 2020

Kungiyar Tarayyar Turai ta nuna fargabarta kan yiwuwar rikici bayan da hukumar zaben kasar ta ayyana Quattara a matsayin wanda ya lashe zabe.

https://p.dw.com/p/3koTu
Elfenbeinküste | Präsidentenwahlen 2020 | Demonstration
Hoto: Sia Kambou/GETTY IMAGES

Dubun dubatar al'ummar Cote d'ivore ne suka fara tsallakewa daga kasar zuwa kasashe makwabata, domin gudun barkewar rikicin bayan zaben da hukumar zaben kasar ta sanar da cewa shugaba mai ci yanzu ne ya lashe shi da gagarumin rinjaye.

Tabbatar da Shugaba Alassane Ouattara a matsayin wanda ya lashe babban zaben kasar karo na 3, a wani kiyasi na hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ya ce hakan ka iya sa akalla mutane 3,200 ne zasu nemi mafaka a kasashe makwabta da suka hada da Togo da Laberiya da kuma Ghana. Mafi yawan masu hijrar sun kunshi mata da yara kanana.

Haka zalika ita ma Kungiyar Tarayyar Turai ta nuna damuwarta dangane da yiyyuwar barkewar rikicin.