Cote d′Ivoire da Ghana za su tabbatar da farashin koko | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 05.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Cote d'Ivoire da Ghana za su tabbatar da farashin koko

Kasashen Cote d'Ivoire da Ghana sun kuduri aniyar cewa su da kansu ne za su tallata su kuma tabbatar da farashin koko. Ana sa rai a kaka mai zuwa farashin tan daya na koko zai kai dala 2600 wato karin kashi 10 cikin 100.

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce kasashen Cote d'Ivoire da Ghana sun kuduri aniyar cewa su da kansu ne za su tallata su kuma tabbatar da farashin koko. Hakan na zuwa ne daidai lokacin da hada-hadar koko da cokulat ke bunkasa amma a hannu daya ana ci da gumin kananan manoman koko. Kawo yanzu kasuwar duniya ke samar da farashin na koko amma ba masu nomansa. Ana sa rai a kaka mai zuwa farashin tan daya na koko zai kai dala 2600 wato karin kashi 10 cikin 100 idan aka kwatanta da farashinsa na yanzu. Ghana da ke zama kasa ta biyu da ta fi noman koko a duniya, da ita da makwabciyarta wato Cote d'Ivoire ke noma kimanin kashi 60 cikin 100 na yawan koko a duniya, abin da ke samar da dala miliyan dubu 100 a shekara, amma manomansa a kasashen guda biyu ba sa cin amfaninsa.

Yayin da kasashen Ghana da Cote d'Ivoire suka dukufa kan samun iko da kasuwar koko da suke nomawa, ita kuwa kasar Angola mai arzikin man fetur, wani muhimmin mataki ta dauka don kawar da nakiyoyin karkashin kasa da har yanzu suke binne a wasu sassan kasar tun lokaci yakin basasan kasar daga shekarar 1975 zuwan 2002. A labarin da ta buga dangane da batun jaridar Die Tageszeitung ta ruwaito gwamnatin Angola na cewa ta ware dala miliyan 60 don gudanar da aikin a gandun dajin Mavinga da Luengue-Luiana da ke a Kudu maso Gabashin kasar, wanda da kuma ke a jerin dazuka mafi daraja a Afirka, da kuma ke kunshe da hallitu da koramu da ke karkashin kariya, amma ke da wuyan shiga saboda nakiyoyin karkashin kasa da ke binne a ciki. Za a dauki tsawon shekaru biyar ana wannan aiki.

Ita kuwa jaridar Der Tagesspiegel a wannan mako ta yi tsokaci ne kan attajirai na nahiyar Afirka tana mai cewa da yawa daga cikin masu arziki a nahiyar Afirka sun tashi ne a cikin talauci, da yawa daga cikinsu yanzu haka suna taimakon talakawa da sauran mabukata. Jaridar ta ruwaito wani nazari da cibiyar Forbes Africa ta yi da ke cewa Afirka na da attajirai a rukunin biloniyas har mutum 20, mafi arziki a cikinsu shi ne dan Najeriyar nan Aliko Dangote, wanda lokaci da yake matashi ya kasance mai tallar alawa a kan titi. Yanzu gidauniyarsa da aka ware wa kudi fiye da dala miliyan dubu daya na taimakawa a fannonin ilimi, fasaha, kananan masana'antu da kuma taimakon jinkai. Jaridar ta ce akwai makeken bambanci tsakanin akasarin 'yan Afirka da attajiran wannan nahiya, sai dai a karshe abokin gabarsu guda ne wato gwamnatoci da suka gaza, musamman matsalar cin hanci da rashawa da rashin iya gudanar da harkokin mulki.