1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cote d'Ivoire bayan zaɓen shugaban ƙasa

November 7, 2010

Bisa ga dukkan alamu za a sake komawa zagayen zaɓen fid da gwani a ƙasar Cote d'Ivoire

https://p.dw.com/p/Q0uW
Alassane Ouattara ɗaya daga cikin 'yan takarar shugaban ƙasa a Cote d'IvoireHoto: AP

A yau zamu fara ne da ya da zango a ƙasar Cote d'Ivoire, inda a ƙarshen makon da ya wuce aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa karo na farko a cikin tarihin demoƙraɗiyyar ƙasar ta yammacin Afirka. A cikin wani rahoton da ta gabatar ƙarƙashin taken: "Lokacin tsage gaskiya ga 'yan Cote d'Ivoire yayi." Jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Zaɓen shugaba na farko da aka yi a demoƙraɗiyance a tarihin ƙasar Cote d'ivoire bai ba da wata takamammiyar nasara ga 'yan takarar ba kuma a sakamakon haka akwai yiwuwar komawa ga zagayen zaɓen fid da gwani tsakanin shugaba mai ci Laurent Gbagbo da abokin takararsa Alassane Ouattara nan da makonni biyu masu zuwa. Matsayin da tsofon shugaba Henry Konan Bedie da ya shugabancin ƙasar daga 1993 zuwa 1999 zai ɗauka shi ne zai taka muhimmiyar rawa a zaɓen na fid da gwani ranar 28 ga nuwamba kamar yadda daftarin tsarin mulkin ƙasar ya tanada."

A saboda ganin da take cewar tana fama da matsin lamba daga 'yan jarida gwamnatin Afirka ta Kudu ke shawarar ƙayyade 'yancin kafofin yaɗa labarai a ƙasar, kamar yadda jaridar Neues Deutschland ta rawaito ta kuma ci gaba da cewar:

"Gwamnati da mahukunta a Afirka ta Kudu na fama da ƙaƙa-nika-yi da rahotanni na zargin cin hanci da ake yaɗawa a kullu-yaumin a ƙasar da kuma ƙorafin facaka da ake wa jami'an siyasa. Wannan shi ne ainihin dalilin da ya sanya gwamnati ke shawarar ƙayyade 'yancin 'yan jarida. To sai dai kuma ƙungiyoyi na farar sun fara bayyana adawarsu da wannan shawara, musamman ma bayan kama ɗan jaridar nan Mzilikazi wa Afrika a farkon watan agustan da ya wuce sakamakon yunƙurin fallasa wata taɓargaza ta cin hanci da yayi."

A can Kenya ma ana fama da fafutukar yakar cin hanci da almubazzaranci na 'yan siyasa a cewar jaridar Süddeutsche Zeitung. Jaridar ta ce:

"A cikin makonni biyu kacal wasu ministocin biyu da sakataren ƙasa da kuma magajin garin Nairobi ko dai sun yi murabus ko kuma an kore su daga bakin aikinsu. Dukkansu ana zarginsu ne da facaka da baitulmalin gwamnati. Ƙasar Kenya dai a halin yanzu haka tana a matsayi na 154 ne a cikin jerin ƙasashen da cin hanci yayi musu katutu a jadawalin ƙungiyar yaƙi da cin hanci ta Transparency International."

A can ƙasar Tanzaniya ma dai an gudanar da zaɓen a ƙarshen mako to sai dai kuma kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta rawaito an shiga tashintashina bayan da sakamako na farko ya nuna cewar shugaba Kikwete dake mulki shi ne ke kan gaba. Jaridar ta ƙara da cewar:

"Wani abin madalla game da zaɓen dai shi ne kasancewar a karon farko an samu zabiya da zai shiga majalisar dokokin Tanzaniya. To sai dai kuma a ɗaya ɓangaren an tsoron ɓillar tashe-tashen hankula irin shigen na Kenya wajejen ƙarshen shekara ta 2007, sakamakon tashintashinar da ake famar fuskanta a birane da dama na ƙasar dake gabacin Afirka."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Halima Balaraba Abbas