1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sallamo Simone Gbagbo daga kaso

Gazali Abdou Tasawa MNA
August 8, 2018

Mahukuntan Cote d'Ivoire sun sallamo a wannan Laraba Simone Gbagbo wacce Shugaba Ouattara ya yi wa afuwa tare da wasu fursunoni 800 a ranar Litinin da ta gabata albakacin zagayowar shekaru 58 da samun 'yancin kan kasar.

https://p.dw.com/p/32qQt
Elfenbeinküste Simone Gbagbo
Hoto: picture-alliance/AP Photo/R. Blackwell

Rahotanni daga kasar Cote d'Ivoire na cewa mahukuntan kasar sun sako Simone Gbagbo uwargidan tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo, wacce Shugaba Alassane Ouattara ya yi wa afuwa a ranar Litinin da ta gabata tare da jerin wasu fursunoni 800.

Lauyan matar ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa an saki Simone Gbagbo mai shekaru 69, a wannan Laraba bayan da ta share shekaru bakwai a tsare a cibiyar horas da jami'an tsaron na jendarma ta birnin Abidjan. Tuni ma ta koma a gidanta da ke a unguwar Cocody ta birnin Abidjan, inda dubunnan magoya bayanta suka shirya mata kasaitaccen tarbo. 

Amma tun a shekara ta 2012, Simone Gbagba na a karkashin sammacin kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya wato ICC da ke nemanta ruwa a jallo. Sai dai Shugaba Ouattara ya sha alwashin da ba zai sake mika wani dan kasar ba a gaban wannan kotu ta duniya wacce ke rike da tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo shekaru da dama.