1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COP23: Shekarar 2017 ta zamo mai zafi

Yusuf Bala Nayaya
November 13, 2017

Kwararru a fannin kimiya sun bayyana cewa sinadaran Carbon dioxide (CO2) da ke haddasa dumamar duniya wanda adadin karuwarsa ke tafiya a kadami guda tun daga 2014 a wannan shekara zai karu da kashi biyu cikin dari.

https://p.dw.com/p/2nXFv
Deutschland Vorbereitungen COP 23 UN-Weltklimakonferenz Bonn
Hoto: picture-alliance/dpa/O. Berg

Kwararrun sun bayyana haka ne a wajen taron sauyin yanayi na COP23 da ke wakana a nan birnin Bonn.

A cewar Corinne Le Quere, kwararriya kan sauyin yanayi kuma darakta a cibiyar bincike kan sauyin yanayi ta Tyndall a jami'ar East Anglia a Ingila kuma jagorar binciken, abin da suka gano abin takaici ne, kuma mafita ita ce bin sharuda da shawarwari da kwararrun ke bayarwa kan kare muhallin.

A cewar kwararrun muddin ana samun tan biliyan 41 na C02 kamar a wannan shekara ta 2017 zai wahala a rage dimamar duniya da digiri biyu da ake fata.