Cocin Katolika ta sami sabon Paparoma | Labarai | DW | 13.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cocin Katolika ta sami sabon Paparoma

A zabe mafi gaggawa a tarihin zaben Paparoma, manyan limaman Cocin sun zabi Paparoma na 266 wanda zai jagoranci mabiya darikar fiye da milliyan dubu guda a duk fadin duniya

White smoke rises from the chimney on the roof of the Sistine Chapel meaning that cardinals elected a new pope on the second day of their secret conclave on March 13, 2013 at the Vatican. AFP PHOTO / ALBERTO PIZZOLI (Photo credit should read ALBERTO PIZZOLI/AFP/Getty Images)

Farin hayaki daga majami'ar Sistine

Kadinal Kadinal na Ekkilisiyar Katolika sun zabi sabon paparoma wanda zai jagoranci mabiya darikar da adadinsu ya wuce milliyan dubu guda a duk fadin duniya.

Jama'a dai sun jinjinawa manyan mallaman Cocin wadanda suka ajiye banbance-banbancensu suka zabi paparoma na 266 a zagaye na biyar, na zabe mafi sauri a tarihin Ekilisiyar.

Dubun dubatan mabiya darikar ne suka yi dandazo a dandalin St Peter lokacin da farin hayakin ya bulbulo kana kuma aka fara kada kararrawar st Peters Basillica, nan da nan kuma mabiyan suka fara kuwan "Habemus Papam!" wanda ke nufin mun sami Paparoma a harshen Romawa na daa wato Latin .

Paparoman wanda ba'a riga an bayyana sunasa ba, zai bayyana a karon farko ta tagar da ke kallon dandalin na St.Peters domin ya yi jawabi ga mabiya darikar ta sa

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Yahouza Sadissou Madobi