Clinton za ta yi takarar shugaban Amirka | Labarai | DW | 13.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Clinton za ta yi takarar shugaban Amirka

Mai dakin tsohon shugaban Amirka Bill Clinton wato Hillary Clinton ta bayyana aniyarta ta tsayawa takarar shugabancin Amirka din karkashin inuwar jama'iyyar Democrat da ke mulki.

A wani sako na bidiyo da ta fidda kan wannan aniya, Ms. Clinton ta ce ta yanke shawarar neman kujerar shugabancin kasar ce don kyautata rayuwar al'ummar kasar.

Cikin watan gobe ne ake sa ran za ta fara yakin neman zabe gadan-gadan da nufin samun sahalewar 'yan jam'iyyarsu ta Democrat a zaben fidda gwani da za a yi.

Ms. Clinton dai wadda tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amirka din ce ta taba neman wannan kujera a 2008 sai dai ba ta yi nasara ba don shugaban kasar mai ci Barack Obama ne ya lashe zaben fidda gwamani na jam'iyyar ta Democrat da aka yi.