1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Cisse ya yi fatali da sakamakon zabe

Yusuf Bala Nayaya
August 13, 2018

Dan takarar jami'iyyar adawa Soumaila Cisse ya ce al'ummar Mali ba za su lamunci murdiyar zabe ta masu mulkin kama karya ba, don haka al'umma "su tashi tsaye".

https://p.dw.com/p/336fa
Porträt - Soumaila Cisse
Soumaila Cisse dan takarar jam'iyyar adawa a MaliHoto: Getty Images/I. Sanogo

Jagoran adawa a kasar Mali Soumaila Cisse ya bayyana a wannan Litinin cewa zai yi fatali da sakamakon zabe zagaye na biyu da aka yi a kasar wanda ya ce cike yake da magudi, ya kuma yi kira ga al'ummar kasar "da su tashi tsaye".

Ya ce sun tabbatar da aikata magudi a zaben don haka ba za su amince da sakamakon ba. Cisse ya bayyana haka ne ga taron manema labarai a hedikwatar jam'iyyarsa da ke birnin Bamako.

Ya ce al'ummar Mali ba za su lamunci murdiyar zabe ta masu mulkin kama karya ba.