Cin zarafin wadanda ake zargi da maita daga Anti-Balaka | Labarai | DW | 26.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cin zarafin wadanda ake zargi da maita daga Anti-Balaka

Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya ya zargi mayakan Kiristoci na Anti Balaka a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da laifin azabtar da wadanda ake zargi da maita.

Wannan rahoto dai da Fondation Thomson Reuters ya samu dubawa, na dauke ne da hotuna na mutanen da aka daure jikin itatuwa ana azabtar da su da wuta, kuma lamarin ya wakana ne tsakanin shekarar 2014 zuwa farkon shekarar wannan ta 2015 wanda shugabannin kungiyar ne ta Anti Balaka suka bada umarnin yin hakan, inda ake kone wasu sassan jikin mutanen kafin daga bisani a biznesu da ransu.

Jamhuriyar Afirka ta tsakiya dai ta fada cikin yanayi na rikicin kabilu da adinai tun bayan da 'yan tawayan Seleka mafi yawansu Musulmai suka kwaci mulki a watan Maris na 2013 a kasar da ke da rinjayan Kiristoci. A ran 27 ga watan Disamba ne dai mai zuwa ake sa ran shirya zaben shugaban kasa a wannan kasa mai fama da tarin rigingimu.