Cin zarafin mutane a Bangui
August 12, 2015Talla
Kungiyar kare hakkin jama'a ta Amnesty International ta ce lamarin ya faru ne a makwan jiya bayan wata takadda da aka samu tsakanin sojojin kiyaye zaman lafiya daga kasashen Kamaru da na Ruwanda da mazauna birnin Bangui. Dama tuni MDD ke binciken batun yin latata da yara wanda aka zargi sojan kasar Faransa da aikatawa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. A yanzu haka MDD na da sojoji kimanin 10.000 da ke aikin raba fada tsaklanin mayakan kiristoci da na musulmai a kasar.