Cin hancin da karɓar rashawa na ƙaruwa a duniya | Labarai | DW | 03.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cin hancin da karɓar rashawa na ƙaruwa a duniya

Ƙasashen Afganistan da Koriya ta Arewa da Somaliya sune ke kan gaban wajen cin hanci a cewar rahoton shekara na Transparency International.

Rahoton ya ce ƙasahen sun yi fice wajen cin hacin yayin da ƙasashen Danmark da New Zeland suka kasance ƙasashen da babu cin hancin so sai. Wannan shi ne irin sakamakon da rahoton shekara da ƙungiyar da ke yaƙi da cin hanci a duniya wato Transparency International ta bayyana ya nunar.

Ƙungiyar wadda ke da cibiyarta a birnin Berlin na nan Jamus, ta ce kusan kishi 70 cikin ɗari na ƙasashen duniya, na fama da babbar matsalar ta cin hanci wadda ta ce babu wata ƙasa daga cikin ƙasashen 177 da ke da kyakyawan sakamako. Kuma ta ce a cikin ƙasashen da aka samu ci gaba wajen yaƙi da cin hanci a kwai Bama, yayin da Iraki da Libiya da Sudan da Sudan ta Kudu da Chadi, suka kasance a sahun ƙarshe da kuma wasu sauran ƙasashen.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu