Cin hanci ya samu gidin zama a kan sha'anin ilimi a Afirka
November 21, 2013Kama daga cinikin na takardun shaida ya zuwa na satar jarrabawa dama na lalata da dalibai dai sannu a hankali dai harkokin ilimi na samun komawa baya a ɗaukacin nahiyar baki ɗaya.
Rahoton ya ambato ƙasashe da dama irinsu Najeriya da Nijar
Rahoton mai shafuka sama da 400 dai ya taɓo matsalolin kama daga na saida takardun jarabawa a jamhuriyar Nijar ya zuwa sace kuɗaɗen kasafin kuɗin ilimi a ƙasar Kenya da kuma ƙaurace war malaman Makaranta a Jamhuriyar Kamaru sannan kuma da uwa uba lalata da ɗalibai 'yan makaranta a Tarrayar Najeriya.Sabon rahoton da ke zaman irin sa na farko da ke nazarin batun na cin hanci a cikin harkar ilimi dai alal misali ya ambato ƙasashen Ghana da Kamaru da Tarrayar Najeriya a matsayin na kan gaba cikin ƙasashen da ɗalibai kan ba da na goro domin samun ilimi a duniya baki ɗaya.Sabon rahoton dai a faɗar Marie- Angie Kalenga da ke zaman babbar jami'ar ƙungiyar da ke kula da yankin yammacin Africa dai na ƙara tada hankali da nuna jan aikin dA ke a gaba a ƙoƙarin nahiyar na wadatar da ilimin al'ummarta.Ta ce:''Rahoton na nuna babu wani sashen na ilimi a nahiyar da ya tsira daga batu na cin hanci .Ko dai a mataki na firamare.''
Shin yaya lamarin yake a Najeriya dangane da rahoton ?
A nan Najeriya da ke masauƙin baƙi dai rahoton na zuwa ne a daidai lokacin da jami'oin ƙasar ke cikin wattanni na biyar ba darasi, a wani abun da ke nuna alamun rushewar tsarin da ƙasar ke dogaro da shi da nufin tabbatar da ci gaban al'ummarta.Tuni dai dama ilimi a mataki na sakandare ya koma na kuɗi inda iyaye kan zaɓi makarantu na kuɗi masu ɗan karen tsada domin tabbatar da samar da cikaken ilimi a cikin ya'yansu.Duk da cewar an kai ga ƙaddamar da makarantun almajirai har ya zuwa yanzu ƙasar ta Najeriya ce ke ta kan gaba ga batun yara ƙanana da basu karatu inda aka tsara sama da yara miliyan 10 na yawo a tituna babu karatu.
Nawani Aboki dai na zaman jagoran wasu kungiyoyin kusan dari biyar na masu zaman kansu. Ya ce: ''ana dai kallon shi kansa batun talauci da rashin tsaron da yai aure yake shirin tarewa a sashen arewacin ƙasar na da ruwa da tsaki da batun lalacewar ilimin a matakai daban- daban.''
Daga ƙasa za a iya sauraron rahoton da wakilinmu a Abuja Ubale Musa ya aiko mana a kan bayyanin da ƙungiyar ta yi, da rahoton wakilinmu na Mina Babangida Jibril da ke yin bita a kan rashin kulawar gwamnati, da Rahoton wakilinmu na Zinder Larwana Malam Hami dangane da yadda ake sayen jarabarwar a Nijar a ƙarshe da kuma rahoton Ibrahima Yakubu dangane da lalata da malamai ke yi da 'yan mata a manyan makarantu.
Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Abdourahamane Hassane