1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na fama da cin hanci

Abdoulaye Mamane Amadou
January 29, 2019

Kungiyar Transparency International mai yaki da cin hanci da rashuwa a duniya, ta koka da yanda cin hanci da karbar rashuwa ke kara samun gindin zama a kasashen duniya musamman a kasar Amirka.

https://p.dw.com/p/3CNqX
USA Krise Shutdown l Präsident Trump verkündet vorläufige Aufhebung der Haushaltssperre
Hoto: picture-alliance/CNP/O. Douliery

A cikin rahotonta na shekara-shekara da ta fitar a wannan Talata, kungiyar ta Transparency International mai cibiya a birnin Berlin na kasar Jamus, ta soki yanda shugaban Amirka Donald Trump ke wuce gona da iri wajen muzguna wa ma’aikatun gwamnati. 

Rahoton ya bai wa kasar Amirka maki 71 cikin 100, inda kungiyar ta ce Amirka ta fuskanci koma baya da maki 4, wanda kuma shi ne karo na farko tun daga shekarar 2011, da kasar ta fita daga cikin ruknin kasashe 20 na farko da suka fi rashin cin hanci a Duniya.

Rahoton ya kara da cewa kashi biyu daga cikin uku na kasashe 180 da ta gudanar da bincike a cikinsu, na fama da matsalar cin hanci da rashawa. 

Kasar Danemark ce dai ke a sahun gaba wajen rashin cin hanci da maki 88, a yayin da kasashen Sudan ta Kudu, Syria da Somalia ke a sahun gaba wajen cin hanci.