Cimma Burin Rayuwa - Samun horo da sanin makamar aiki | Learning by Ear | DW | 16.07.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Learning by Ear

Cimma Burin Rayuwa - Samun horo da sanin makamar aiki

default

Cimma Burin Rayuwa - Samun horo da sanin makamar aiki.

Tun daga kan malamin makaranta, bakanike, mai gyaran motoci, manomi ko kuma ɗan Jarida, akwai damar samun ayyukan yi a nahiyar Afirka, amma kash! mutum fa sai ya yi da gaske a ɗauke shi aiki saboda ƙarancin guraben yin aikin.

Shirin Ji Ka Ƙaru ya yi tanadin hanyoyin da za a bi a biya muku buƙata ta samun aikin da ya dace da ku.

Wane aiki ne ya dace da ni? A lokatai da dama mutum kan rasa abin da yake so ya yi saboda rashin masu ba shi shawara, to amma ƙwararrummu masu ɗauko mana rahotanni sun gana da jama’a daban-daban sun kuma tattauna dasu domin su taimaka musu da irin abubuwan da suka dace da su ta ɓangaren aikin yi. Misali kana son ka zama makaɗi ne ko kuwa ma’aikacin hotal, za su nuna abin da zai karɓe ka in kana son zama malamin makaranta ko masanin na’ura mai kwakwalwa.

Ka- Iso

Za a riƙa kawo muku rahotanni na musamman wanda za ku amfana da su, kamar yadda za ku samu guraben ƙaro ilimi a Jami’o’i da yadda za ku iya samun aiki ba fargaba, dama yadda ake samun hanyar biyan kuɗin makaranta da yadda za ka iya zama da sauran ɗalibai.

Sahihan Bayanai da Annashuwa

Banda hirarraki da za a riƙa kawo muku na jama’a daban-daban akan ayyukansu, Shirin Ji Ka Ƙaru zai kawo muku wasu shirye-shirye na wasan kwaikwayo. A irin wannan wasan za mu bi wata yarinya budurwa, wadda ta bar Ƙauye ta je neman ilimi a birni, da burin samun takardar shaida a fannin aikin gona. Za mu ga irin gwagwarmaya da matsaloli da ta fuskanta.

An yi shirin na Ji ka ƙaru a harsuna shidda, waɗanda suka haɗa da Ingilishi, Kiswahili, Faransanci, Hausa, Portuguese, da Amharic.

Shirin Ji Ka Ƙaru na samun gudunmuwa ne daga ofishin hulɗa da ƙasashen waje na ƙasar Jamus.

Sauti da bidiyo akan labarin