Cika shekaru biyu da hawan mulkin shugaba Issoufou na Nijar
April 7, 2013A jamhuriyar Nijar a ranar bakwai ga watan Afrilu aka yi shagulgulan bikin zagayowar shekaru biyu da hawan mulkin shugaban kasar Alhaji Mahamadou Isoufou. Albarkacin zagayowar wannan ranar, shugaban ya yi wa al'umma kasa jawabi, inda ya yi bitar aikin da ya yi na cika alkawuran da ya dauka.
Batun tsaro shi ne goshin jawabin da na sa, inda ya ce gwamnatinsa ta yi kokarin tabbatar da tsaro cikin gida, waje, bayan tashe-tashen hankulan da suka taso a cikin kasashen da makwabtan Nijar. Kasar da na cikin sahun kasashen da suka aika dakaru Mali, don fatattakar masu kishin addini da suka mamaye arewacin kasar. Bagu da kari gwamnatinsa ta dau matakin bai wa dakarun Nijar kayan aiki don kare iyakar kasar da kuma tabbatar da tsaro cikin gida. A tsari sa na dan kasa ya ci da dan kasa, shugaban ya ce gwamnatinsa na kokarin bunkasa noman fadama da kuma kiwon zamani ta yadda za a sami isasshen abinci. Kiwon lafiya da bunkasa ilimi da wadatar da ruwan sha gwamnatinsa na cikin cika alkawalin da ta dauka. A fannin hako ma'adani na karkashin kasa, tun lokacin da aka fara hako man fetur, an sami rarar kudi CFA miliyan dubu tasa'in da biyar. Wajen fara babban aikin hako karfen uranium a Umiraren wanda zai fara a 2015.
Rashin gamsuwa da wannan mulki
A nasu wajen 'yan adawa sun bayyana cewa tsawon shekaru biyu da shugaba Issoufu, ya yi a kan mulki bai yi wani aiki na a zo a gani ba. Mahaman Murtala, wani jigo a jam'iyar MNSD adawa, yace "batun tsaro dai babu wani ci gaba, inda ya musanta cewa ana ba duk soja tufafi kaya uku, ko kusa ba haka ba ne, daya ne ake ba ko wane soja. Sabanin mulkin tsohon shugaban kasa Tanja Mahamadou."
Murtalan ya ci da cewa gidajen asibitocin Nijar akwai matsaloli ga tsadar rayuwa, inda a yanzu ake sayar da buhun gero kudi CFA 30.000. Abinda ba a taba gani a Nijar ba.
A bangaren musu mulki a cewar Alhaji Adaye, mashawarci a fadar shugaban kasa, shi ganau ne ba jiyau ba alkawuran da shugaba ya dauka ya na cikasu.
"Can jihar Tahoua an sa mutanen kasar China, suna aikin saka fonfunan ruwa cikin karkara."
Har yanzu wasu ba su gani a kasa ba
To amma a bangaren ma'aikata sun bayyana rashin cika alkawarin wannan gwamnati tun hawan shugaba Mahamadou Issoufou. Kawancen mayan kungiyoyin kwadago wadanda suka yi gwagwarmayar kawo goyon bayan gwamnatin jamhoriya ta bakwai sun fiddo sanarwar sukan lamiri da kakkausar murya. Isoufu Sidiben shi ne babban sakataren babbar kungiyar dake jagoran kawancen kungiyoyin cewa yayi.
"A cikin shekaru biyu sun sa hannu an kulla yarjeniyoyi biyu amma ba su biya musu bukata ko daya ba. Kuma ba don sun yi zaman kawo ma wannan gwamnatin goyon baya ba, za su juya su yadda suka ga dama."
Mawallafi: Mahaman Kanta
Edita: Mohammad Nasiru Awal