Cigaba da zaman sojin Amirka a Afganistan
August 22, 2017Talla
A cikin wani jawabi da ya gabatar a jiya Litanin Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa ficewar sojojin Amirka daga Afganistan na iya kasancewa wata babbar dama ta yaduwa da ma bunkasar kungiyoyin 'yan ta'adda irin su Al-Qaida da IS a cikin yankin. Bugu da karin Shugaba Trump ya ba da umurnin aikawa da karin sojojin Amirka dubu uku da 900 baya ga wasu sama da dubu takwas da ke girke a kasar.
Sai dai tuni kungiyar Taliban ta mayar da martani a game da wannan aniya ta Amirka, inda ta ce matsawar za a samun sauran sojin Amirka ko da daya ne a cikin Afganistan, to kuwa su ba za su fasa yakarsu ba a kan hanyar Jihadi. Akan haka ne ta yi ikrarin daukar alhakin wani hari roka da aka yi zuwa ofishin jakdancin Amirkar a birnin Kabul a jiya Litinin.