Yara 20,000 aka shigar yaki a 2020
June 22, 2021Talla
Rahoton ya ce adadin yara 19,379 suka shiga yanayin tasku a kasashe 19 da ake tarzoma, inda aka kiyasta yara 8,521 aka shigar yaki, an kuma kashe kusan yara kanana 3,000 tare da jikkata wasu sama da 5,000 a fagen daga a shekarar bara.
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ja hanklain mahukunta a kasashen da aka fi samun tashe-tashen hankula, da su ja damara na takaita hare-hare kan kananan yara a makarantu da cin zarafin mata musamman kananan yara.