Ci gaban ziyarar Paparoma a Korea ta Kudu | Labarai | DW | 15.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban ziyarar Paparoma a Korea ta Kudu

A ziyarar da ya ke ta kwanaki biyar a Korea ta Kudu, Paparoma Francois ya yi kira ga al'ummar wannan kasa da ta yi yaki da yanke kauna a cikin zaman rayuwa.

Paparoma ya ce batun yanke kauna cikin yanayi na rayuwa tamkar wata guba ce dake cinye zuciya sannu a hankali. Ya kuma ya jagoranci wani babban zaman taron addu'o'i da aka shirya a wani filin kwallon kafa na birnin Daejeon dake tsakiyar wannan kasa, yayin da aka yi wa daruruwan itace ado da kyallaye masara, a wani mataki na tunawa da daruruwan mutanen da suka rasu a cikin wani jirgin ruwa a watan Afrilu da ya gabata, wadanda akasarin su 'yan makaranta ne. Kazalika ya kuma samu ganawa da iyayen yaran da suka rasu, da ma wadanda suka samu tsira daga hadarin jirgin ruwan.

Paparoma Francois, ya yi kira ga mabiya darikar da su karfafa karfin imani a zukatan su domin a cewarsa, shi kansa imani wani babban magani ne na yawan tunanin dake haddasa yanke kauna a rayuwa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohamed Abubakar