Ci gaban matan Afganistan | Zamantakewa | DW | 29.12.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ci gaban matan Afganistan

A ƙasar Afganistan idan akwai abu guda da ya samu ci gaba bayan mulkin Taliban, shine 'yancin mata, inda suke taka rawa a siyasar ƙasar.

Siddiqa Mobarez 'yar majalisar dokokin Afganistan

Siddiqa Mobarez 'yar majalisar dokokin Afganistan

A zamanin da Taliban ke mulkin ƙasar Afganistan mata basu da sakat, ba'a barin su shiga makarantu balle su yi aikin gwamnati. A shekara ta 2005 an yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima, inda aka ware wasu muƙamai ga mata. A yanzu haka mata ne ɗaya bisa huɗu na 'yan majalisar dokokin ƙasar ta Afganistan, haka zalika mata ne kashi talatin cikin ɗari a majalisun dokokin jihohin ƙasar. To cin ko wane ci gaba matan a ƙasar da yaƙi ya ɗai-ɗaita suka samu........

Izuwa yanzu kusan a ko wacce rana, matan Afganistan na bayyana a gidajen talavijin inda suke bayyana matakan inganta dimokradiyya. Sakina Husein ɗaya ce daga irin matan. Yar shekaru 30 da haifuwa wakiliya ce a majalisar dokokin jahar Herat dake yammacin ƙasar ta Afganistan.

"Mata da kuma 'yan matan da iyayen su, suka kasance masu tsanin kishin addini. Ayyukan ta'addanci ya mai da rayuwarsu baya. 'Yan ƙasar mu suna buƙatar samun gudumawar da irin waɗannan mata yaka mata su bayar"

A majalisar dokokin ƙasar ta Afganistan mai kujeru 249 an ware wa mata kujeru 68. Bayan zaɓen watan Satunban bana, mata 69 suka samu wakilci a majalisar, wato har sun haura kujerun da aka ware musu. Siddiƙa Mobarez sau biyu tana cin zaɓen majalisar dokoki, kuma a gare ta, hakan wani ci gaba ne ga matan Afganistan..

"Idan mace za ta iya kula da iyalinta, to kuwa za ta iya kula da al'umma. Idan ta yi aikin zaɓe, to kuwa za ta tabbatar da cewa mata sun samu nasara. Wannan ya nuna cewa matan a shirye suke, kana su abun yardane. Muna da ƙwarin gwiwa kuma so muke mu kawo sauyi"

Kalmar kawo sauyi dai ita ce aksarin mata suka rubuta a postocin neman zaɓensu. Fiye da mata 400 suka shiga takara a zaɓen majalisar dokokin ƙasar da ya gabata, hakan yanuna ƙarin kashi 70 cikin ɗari fiye da shekaru biyar na baya. 'Yan matan ƙasar sun ƙara yunƙuri a siyasar ƙasar, inda suke fafitikar yaƙi da cin zarafin mata, da nuna musu wariya.

"Zan sake zama cikin al'ummar da babu banbanci tsakanin wani da wani. Ina son ganin an samu al'ummar da babu banbancin tsakanin na miji da mace, ko ƙabila, kuma babu banbacin yare"

A ƙasa irin ƙasashe kamar Afganistan da take da al'adu masu ƙarfi, da kuma kasancewar ta ƙasashe da addini ke taka mahimmiyar rawa, za a ɗauki shekaru kafin a samu dai daito tsakanin al'umma, amma dai ko ba kamai, sauyin da aka fara gani ta ɓangaren mata wani ci gabane matuƙa.

Mawallafa: Usman Shehu Usman da Humaira Haidari

Edita: Umaru Aliyu