Ci gaba taron shugabannin Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 10.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba taron shugabannin Afirka ta Tsakiya

Shugabannin kasashen yankin Afirka ta Tsakiya na ci gaba da gudanar da taron neman warware rikicin da ake samu a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Akwai karin matsin lama kan neman shugaban kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Michel Djotodia ya ajiye aiki, saboda yadda ya kasa taka rawar kawo karshen rikicin da ake samu.

Taron shugabannin kasashen yankin da ke gudana a kasar Chadi, ya gayyato 'yan majalisar dokokin kasar 135, domin samun matsaya ta karshe.

Bisa yarjejeniyar da ta kafa gwamnatin wucin gadi duk wani sauyi sai da izimin 'yan majalisar. Shugabannin kasashen na yankin tsakiyar Afirka suka taimaka aka kafa gwamnatin wucin gadin ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya karkashin Michel Djotodia, cikin shekarar da ta gabata ta 2013. Amma yanzu yana karkashin matsin, saboda yadda rikici mai nasaba da addini ya reitsa da kasar, abin da ya tilasta wa kusan mutane milyan guda tserewa daga gidaje.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu