1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da zanga-zanga a Amirka

December 6, 2014

Dubun-dubatan masu zanga-zanga ne suka yi ddan-dazo a birane daban-daban na Amirka a daren kwana na uku na nuna bacin ransu da yawan kashe bakaken fata a kasar.

https://p.dw.com/p/1E07U
Hoto: Reuters//Elizabeth Shafiroff

Masu zanga-zangar dai na zargin mahukuntan kasar da kin daukar ko wanne mataki bisa kisan bakaken fata da jami'an 'yan sanda farar fata ke yi a Amirkan, bayan da wani alkali ya wanke jami'an 'yan sandan da suka kashe wani bakar fata mai suna Eric Garner a birnin New York, inda ya ce ba zai tuhume su da aikata laifin kisan sa ba. 'Yan san dan dai sun cafke Garner ne bisa zargin sa da sayar da taba ba bisa ka'ida ba, rahotanni sun nunar da cewa sun kama shi ne ba tare da yana dauke da ko wane irin makami ba kafin daga bisani su kashe shi. Dama dai a kwai wata jikakkiya a kasa bayan da alkalin da ke sauraron shari'ar jami'in dan sandan da ya kashe wani bakar fata mai suna Michael Brown a Ferguson na Amirkan a makon da ya gabata ya wanke shi daga zargin yin kisan kai da gan-gan.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman