1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da yin matsin lamba ga Rasha

March 27, 2014

Amirka da kasashen yamma sun sha alwashin ci gaba da takura wa Rasha a kan abun da suka kira da mamaye yankin Kirimiya na kasar Ukraine da ta yi.

https://p.dw.com/p/1BWUJ
Hoto: Reuters

Shugaban kasar Amirka Barack Obama ya bukaci takwarorinsa kasashen yamma da su ci gaba da matsa wa Rasha lamba a kan rikicin kasar Ukraine da ya yi sanadiyyar komawar yankin Kirimiya na Ukraine din karkashin ikon Rashan. Obama ya ce dole ne a nuna wa Rasha cewa amfani da karfin soja ba ya sanyawa a samu riba sai dai ta hanyar maslaha inda ya ce....

"In har wani daga cikin mahukuntan Rasha ya yi tunanin cewa babu wanda zai damu da matakin da suka dauka a Ukraine daga bangaren kasashen Tarayyar Turai da kuma Amirka lallai ya yi kuskure, har yanzu akwai sauran dama ga Rasha ta tattauna da mahukuntan Ukraine da kuma al'ummomin kasa da kasa domin magance lalacewar al'amura, wannan ita ce kadai hanyar da za a iya magance matsalar".

Shugaba Barack Obama dai ya isa kasar Italiya inda zai yi ganawarsa ta farko da Paparoma Francis tare kuma da tattaunawa da sabon Firaminstan Italiya Matteo Renzi da Shugaba Giorgio Napolitano. Ana sa ran Obama zai tattauna da Paparoma Francis a kan batun yakin Siriya da rikicin Isra'ila da Palasdinawa da na Ukraine da ma halin da ake ciki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da rikicin addini ya dai-daita.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal