1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Hamas da Isra'ila

August 8, 2014

Hukumomin Masar sun sanar da cewar ana samun ci gaba a tattaunawar da ake yi dangane da kokarin wanzar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Hamas.

https://p.dw.com/p/1CrSi
Kerry mit Shukri in Kairo 22.07.2014
Hoto: Reuters

Ma'aikatar harkokin wajen Masar din da ta tabbatar da wannan labarin ta ce bangarorin biyu sun amince kan abubuwa da dama inda ta nemi Isra'ila da Hamas su amince da wata sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki uku.

To sai dai a daura da wannan, kungiyar Hamas da dakarun Isra'ila sun ci gaba da kaiwa juna farmaki inda rahotanni ke cewar hakan ya yi sanadiyar rasuwar wani yaro dan shekara goma da kuma jikkata wasu sojin Isra'ila biyu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Suleiman Babayo