Ci gaba da kisan mutane a Kwango | Labarai | DW | 24.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da kisan mutane a Kwango

Rahotanni daga Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango na nuni da cewa an kashe wasu mutane biyar har lahira cikin dare a yankin Beni da ke gabashin kasar.

Yankin na Beni dai na zaman wani sashe da 'yan tawayen kasar Uganada ke da karfi. Shugaban yankin na Beni Amisi Kalonda ya shaidawa manema labarai cewa an dad-datsa mutanen ne da adda, sai dai ya ce bashi da wani karin bayani kan kisan nasu. Kisan mutane da adda a garin na Beni dai na neman zama ruwan dare a watannin baya-bayan nan yayin da ake dora alhakin yinsa a kan 'yan tawayen kasar Yuganda da ke nuna adawa da gwamnatin Shugaba Yoweri Museveni na Yuganda.