Ci gaba da farautar maharan Mali | Labarai | DW | 27.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da farautar maharan Mali

Jami'an tsaron Mali sun cafke wasu mutane biyu da ake kyautata zaton suna da hannu cikin harin da aka kai a Otel din Radisson Blu da ke Bamako babban birnin kasar.

Otel din Radisson Blu Bamako Mali da ya fuskanci harin ta'addanci

Otel din Radisson Blu Bamako Mali da ya fuskanci harin ta'addanci

Rahotanni sun nunar da cewa jami'an tsaron na zargin mutanen biyun na cikin wadanda suka kai hari tare da yin garkuwa da mutane 140 a cikin Otel din, wanda kuma kawo yanzu aka tabbatar da cewa yawan wadanda suka mutu yayin arangamar da aka yi tsakanin jami'an tsaron da maharan ya kai 20. A makon da ya gabata ne dai wasu mutane dauke da bindigogi suka kai hari a Otel din na Radisson Blu da ke Bamako babban birnin kasar Mali wanda baki 'yan kasashen ketare ke sauka. Tuni dai mahukuntan kasar suka sanya dokar ta baci ta tsahon kwanaki 10 domin ba wa jami'an tsaro damar farautar wadanda ake zargi da hannu a harin.