Ci gaba da binciken gawarwakin AirAsiya | Labarai | DW | 31.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da binciken gawarwakin AirAsiya

Rashin kyawun yanayi na kawo nakasu a kokarin da ake yi na lalubo gawarwakin mutanen da ke cikin jirgin saman AirAsiya da ya yi hadari a kasar Indonesia.

Masu aikin ceto sun samu nasarar gano wasu daga cikin gawarwakin wadanda hadarin ya rutsa da su a jirgin saman kirar QZ 8501 da ke kan hanyarsa ta zuwa Singapore daga kasar Indonesiya dauke da mutane 162 da suka hadar da fasinjoji da kuma ma'aikatan jirgin. Jirgin na AirAsiya dai ya fada tekun Java ne sakamakon rashin kyawun yanayi. A cewar Tim van Beveren kwararre a kan harkar jiragen sama, wannan bashi ne karo na farko da aka fuskanci irin wannan matsalar ba.

Ya ce: "Wannan jirgin sama ne na zamani, mun ga makamantan irin wannan matsalar inda wasu na'urori a jikin jirgin za su ki yin aiki yadda ya kamata. Wannan wani abu ne da ya kamata mutane su yi la'akari da shi, a yanzu dai muna fatan samun akwatunan nadar bayanan jirgin wato black boxes."

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu