1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chavismus ohne Chavez

March 6, 2013

Yayin da ake zaman makokin mutuwar shugaban Venezuela Hugo Chavez, wani abin da ke daukar hankali a birnin Caracas, shi ne ci-gaba da bin manufofinsa na siyasa.

https://p.dw.com/p/17sT8
Supporters of deceased Venezuelan leader Hugo Chavez carry pictures of Chavez as they react while his coffin is driven through the streets of Caracas, March 6, 2013. Venezuela's late President Chavez died on Tuesday of cancer, and authorities have not yet said where he will be buried after his state funeral on Friday. REUTERS/Carlos Garcia Rawlins (VENEZUELA - Tags: POLITICS OBITUARY)
Hoto: REUTERS

Tsawon watanni uku kafafan yada labaru da 'yan adawa ke saka ayar tambaya ko Hugo Chavez na nan da ransa. Sai a ranar Talata da yamma Nikolas Maduro, mataimakin shugaban kasa kuma mutumin da Chavez ya nada a matsayin magajinsa ya tabbatar da mutuwar shugaban na Venezuela. Dole Nikolas Maduro ya shirya sabon zaben a cikin kwanaki 30 masu zuwa. Ba wanda ke shakka game da shirya sabon zaben, inji Leslie Wehner dan kimiyyar siyasa a cibiyar nazarin siyasa ta Jamus wato Giga dake birnin Hamburg.

"Za a gudanar da zabukan nan gaba kadan, gwamnati dake ci za ta iya yin amfani da sunan Hugo Chavez don cimma burinta. Chavez ya nada Nikolas Maduro a matsyin gajinsa, kuma ina gani hakan zai taka muhimmiyar rawa a zaben."

Tsarin jamhuriya mafi dadewa

Shi kuwa Stefan Rink na jami'ar birnin Berlin saka ayar tambaya yayi musamman game da kasashen Latunamirka.

Venezuela's Vice President greets supporters during a rally in Caracas February 27, 2013. Venezuelans are commemorating the 24th anniversary of the social uprising known as 'Caracazo' which President Hugo Chavez said marked the start of the his revolution. Results from surveys showed that if Chavez is forced out due to cancer, his preferred successor Maduro is favored to win an election. REUTERS/Carlos Garcia Rawlins (VENEZUELA - Tags: POLITICS ANNIVERSARY)
Nicolas Maduro, mutumin da zai gaji ChavezHoto: Reuters

"Ba Venezuela kadai ba, ilahirin kasashen Latunamirka kasashe ne masu dadadden tsarin jamhuriya a duniya baki daya, duk da mulki na kama karya da a rika samu. Saboda wannan dalili duk wata gwamnati ka iya tabbatar da sahihancinta ba tare da la'akari da kundin tsarin mulkin kasa ba."

Sai dai Jose Colina shugaban kungiyar 'yan kasar Venezuela da suka yi kaura kuma ke da mazauninta a birnin Miami na kasar Amirka, ya ce shin kam ba zai amince da wannan gwamnati ba.

"Ai ba wanda ya rantsar da Hugo Chavez da ilahirin majalisar ministocinsa da kuma Nicolas Maduro. Saboda haka wata haramtacciyar gwamnati ta yi amfani da haramtattun dokoki ta halasta wata gwamnati."

Magudi a zaben shekarar 2012

Tun a zaben da aka yi baya bayan nan an yi amfani da kudin kasa da kafofin yada labaru a hanyoyin da ba su dace ba, sannan a wasu wuraren an tursasa wa masu zabe. Masana na zargin cewa jam'iyar Hugo Chavez za ta yi aringizon kuri'u a zaben dake tafe, domin ci-gaba da aiwatar da akidar marigayin. Ko da yake Maduro ba ya da kwarjini kamar Chavez amma a matsayin tsohon direban bas kuma dan kwadago yana da abubuwan da zai iya yin gadara da su, kasancewa lokacin da yake rike mukamin ministan harkokin waje yayi biyayya tare da yin aiki tukuru.

U.S. President Barack Obama (L) greets his Venezuelan counterpart Hugo Chavez before the opening ceremony of the 5th Summit of the Americas in Port of Spain in this April 17, 2009 file photo. Chavez has died after a two-year battle with cancer, ending the socialist leader's 14-year rule of the South American country, Vice President Nicolas Maduro said in a televised speech on March 5, 2013. REUTERS/Miraflores Palace/Handout/Files (TRINIDAD AND TOBAGO - Tags: POLITICS OBITUARY) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS
Hoto: Reuters

Sai dai su ma 'yan adawa ka iya taka rawar gani idan suka hada kai, kamar yadda suka yi a zaben karshen shekarar 2012, inda suka tsayar da dan takara guda.

Mawallafa: Jan D. Walter / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe