1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba a kokarin warware rikicin arewacin Mali

January 12, 2013

Wasu kasashen ECOWAS da kuma Amurka sun bi sahun Faransa wajen bayar da gudunmwar sojoji da makamai domin yakar masu kishin Islama a arewacin Mali.

https://p.dw.com/p/17Iwm
Mali Bamako SoldatenHoto: Reuters

Kasar Faransa ba ta fito fili ta baiyana irin rawar da za ta taka a yakin da ake yi da masu kaifin kishin addinin Mali ba. Sai dai ministan harkokin wajen ta Laurent Fabius ya nunar da cewa sojojinsu za su kai samame ne ta sama. Da ma dai kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa Faransa ta jibge jiragen yakinta da kuma masu saukar angula a kasar ta Mali. Yayin da a daya hannun kuma ta tura da tarin sojojinta na kundunbala. Tuni dai shugaba Dioncounda Traore ya riga ya yi kira ga 'yan Mali da su fito su kare kasarsu daga mamayar masu kaifin kishin Islama.

GettyImages 158217193 Mali's interim government President Dioncounda Traore makes a statement in Bamako on December 11,
Shugaban Traore ya nemi 'yan Mali su kare kasarsuHoto: AFP/Getty Images

"Gwamnatin Mali ta yanke shawarar kafa dokar ta baci. Dole kowace 'yar Mali da kuma kowane dan Kasa ya dauki kan shi a matsayin soja. Sannan kuma ya fito ya nuna kishin kasa."

Kasashen da za su bayar da gudunmawa a Mali

Shugaban na Mali ya kuma kara da cewa kungiyoyin da ke da kaifin kishin addinin ne suka zarta makadi da rawa. saboda haka ne rundunar sojojin kasar ba za su nuna sani ko sabo ba. Baya ma dai da taimakon sojojin Faransa, gwamnatin Amurka ma za ta taimaka da jiragen da ke sarrafa kansu da kansa wadanda za su yi shawagi a sararrin samaniyar Mali. Su ma dai wasu kasashe mambobin ECOWAS ko CEDEAO sun yi alkawarin bayar da gudunmawar sojoji. Babban jami'i zartaswa na ECOWAS ko CEDEAO, Kadré Désiré Ouedraogo ya nunar da cewar adadin sojojin zai iya kaiwa 3000.

"Za su isa Bamako a kowane lokaci daga yanzu. Wadanda za su jagorancin rundunar za su isa a karshen mako. Yayin da su kuma sojojin za su fara kai sumame a farkon mako mai zuwa. Daukacin kasashen ECOWAS ko CEDEAO ne ya kamata su bayar da gudunmawar sojoji. Amma kuma salon da rikicin ya dauka ya sa kasashe hudu sun gaggauta turo da nasu kason. Domin hana tabarbarewar al'amuran tsaro ne ya sa ECOWAS ko CEDEAO ta yanke shawarar sa baki."

(
Ouedraogo ya ce ECOWAS za ta tura da sojoji 3000 MaliHoto: picture-alliance/dpa

Barazanar kungiyar Ansr Dine ga kasar Faransa

Tun dai a karshen watan disemba ne kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince a afkawa masu kaifin kishin islama da yaki domin a fatattakar su daga arewacin Mali. Sai dai kuma wasu matsalolin siyasa da kuma na kayan yaki da aka fuskanta, sun hana aiwatar da shirin cikin hanzari. Faransa ita ce kasar farko da ta dogara kan kudirin Majalisar Dinkin Duniya wajen taimaka wa sojojin Mali yakar masu kishin Islama. Sai dai yunkurin na François Holland na tattare da hadari, saboda kungiyoyi na ci gaba da garkuwa da wasu 'yan kasarsa. Tuni ma dai Sanda Ould Bouamama, kakakin kungiyar Ansar Dine ya yi barazanar mayar wa Faransa da martani

"Faransa za ta dandana kudarta. Mu ba malalata ba ne. Ba mu da jirage da kuma makamai. Amma kuma muna da karfin imani. Wannan ne zai sa mu ci galaba."

Symbolbild Rebellen Mali Timbuktu Weltkulturerbe zerstört
Ansr Dine ta yi barazanar rama wa Faransa aniyartaHoto: dapd

Nasara guda da ta fito fili ita ce ta kaurajinin shugaba François Hollande da ya karu a tsakanin talakawan Mali. Rahotanni sun nunar da cewa 'yan Mali da dama sun kawata motocinsu da tutar kasar Faransa domin nuna jin dadinsu game da gudunmawar sojoji da ta bayar.

Rahoto cikin sauti kan ci gaban da aka samu a Mali na kasa

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Saleh Umar Saleh