Chaina ta tura sojoji iyakar Hong-Kong | Labarai | DW | 13.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chaina ta tura sojoji iyakar Hong-Kong

Shugaba Trump na Amirka ya sanar da cewa kasar Chaina ta soma girke sojoji akan iyakarta da Hong-Kong inda zanga-zangar neman sauyi ke ci gaba da kamari

Shugaba Trump na Amirka ya sanar da cewa Chaina ta soma girke sojoji akan iyakarta da Hong-Kong inda zanga-zangar neman sauyi ke ci gaba da yin kamari. Shugaba Trump ya sanar da hakan ne a wani sakon Twitter inda ya yi kira ga bangarorin da ke rikici a Hong-Kong da su bi hanyar laluma wajen warware rikicin. Ya kuma bayyana fatan ganin ba za a kashe ko da mutum daya a cikin rikicin a nan gaba ba.

Wannan na zuwa ne a daidai loakcin da 'yan sandan kwantar da tarzoma a Hong-Kong suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar neman sauyi da ke zaman dirshan a filin jiragen saman birnin.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa 'yan sandan sun yi amfani da barkonon tsohuwar domin tsira daga kofar raggon da wasu daruruwan masu zanga-zangar suka yi wa motarsu da ke rakiyar wata motar asibiti. 'Yan sandan sun kuma kama akalla mutane biyu daga cikin masu zanga-zangar wadanda ke ci gaba da dagula harkokin sufuri a filin jirgin saman birnin na Hong-Kong.