Tattalin arziki
Chaina ta saka kudaden fito ga kayayyakin Amirka
May 13, 2019Talla
An samu faduwar kasuwar hannun jari a kasar Amirka a wannan Litinin abin da ke zama makonni biyu a jere ke nan sakamakon cece-kucen kasuwancin da ke wakana tsakanin kasar ta Amirka da kuma Chaina.
Rikicin ya shiga sabon mataki sakamakon martanin da Chaina ta mayar da zai fara aiki a farko watan gobe na Yuni na kakaba kudaden fito ga kayayyakin da za su shiga kasar daga Amirka. Tun farko Shugaba Donald Trump na Amirka ya dankara kudaden fito ga kayayyakin da ke fitowa daga Chaina. Duk bangarorin biyu sun nuna alamun duk da halin da ake ciki za su koma kan teburin tattaunawa ranar Jumma'a mai zuwa.