Chaina ta dauki hankalin kasashen Turai | Labarai | DW | 04.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chaina ta dauki hankalin kasashen Turai

A wannan Talata shugaban kasar Chaina Xi Jinping ya isa kasar Portugal a ziyarar kwanaki biyu da ya ke a kokarin karfafa kyakyawar dangantaka ta kasuwanci da tuni ke fuskantar suka daga kasashen Turai.

Shugaban zai gana da takwaransa shugaba Marcelo Rebelo de Sousa inda ake sa ran su rattaba hannu kan wasu kwangiloli da suka kunshi samar da saukin sufuri da Chainan ta yi wa lakani da 'Silk Road' Shirin ya kunshi bai wa Portugal rancen kudi,  don ta sami daman gina hanyoyi na jiragen kasa da tashoshin jiragen ruwa da kuma wasu sabbin hanyoyi da za su kawo saukin zirga zirga a tsakanin kasar da sauran kasashen yankin Asiya da Turai ya zuwa Afirka.

Shugaba Xi Jinping ya jaddada mahinmancin dangantaka a tsakanin kasashen biyu duk kuwa da suka da ya ke sha daga wasu kasashen Turai da ke kallon matakin na Chaina a yunkuri na son mamaye duk wasu lamura na kasuwanin yankin.