Jagorar yankin Hong Kong ta fidda sanarwar gaggawa
September 3, 2019Talla
Da take kare kare kanta gwamnatin Chaina ta bakin kakakinta Xu Luying ta tabbatar da cewar kasar ta shirya tsaf don daukar matakin magance rikicin siyasar da ya tasamma ruguza yankin na Hong Kong, kodayake kasashe da dama sun zargi mahukuntan Chaina da hannu cikin wannan rikici a baya. Wani rukunin na 'yan kasuwa daga cikin masu zanga-zangar a Hong Kong sun zargi jagora Lam da yaudara, bayan daliban jami'a sun dauki matakin dakatar da zuwa makaranta har na tsawon makwanni biyu .
Yanzu haka 'yan Sandan yankin na tsare da mutanen da yawansu ya kai dubu 1,100 wadanda suka hada da yan siyasa tun daga watan Yunin da ya gabata.