Ceto birran Afirka daga barazanar bacewa
July 25, 2017Talla
Masana kimiyyar halittar birrai kimanin 150 daga kasashen Afirka daban-daban na gudanar da wani taro a birnin Abidjan na kasar Cote D'Ivoire domin kafa wata kungiya da nufin ceto birrai daga barazanar karewa a Afirka.
Masana dai sun bayyana cewa sama da kashi daya daga cikin biyu na nau'o'in birran Afirka na fuskantar bacewa daga doron kasa inda alal misali a Madagascar adadin goggwan biri da ke da akwai a kasar ya ja baya da kusan kashi 90% a shekaru 20 na baya bayan nan.
Birran Afirkar dai na fuskantar barazanar karewa ne a sakamakon ayyukan dan Adam da ke farautarsu da lalata dazzuka da kisan itatutuwa da ke zama muhallansu domin fadada filayen noma ko hakar ma'adanai ko kuma gina birane.