Cece-kucen siyasa tsakanin alkalai da minista a Jamhuriyar Nijar | Siyasa | DW | 22.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Cece-kucen siyasa tsakanin alkalai da minista a Jamhuriyar Nijar

Takaddama ta barke tsakanin bangaren shri'a na Jamhuriyar Nijar da ministan harkokin cikin gida

A Jamhuriyar Nijar wata sabuwar badakala ce ta barke tsakanin babbar kungiyar alkalai ta kasar SAMAN da ministan cikin gida Malam Hasumi Masa'udu kuma sakataren jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki. Alkallan zargin Ministan na cikin gida ne da yi masu katsalandan a cikin zartar da aikin shari'a bisa dalilin ne suka shigar da kararsa domin yi masa hukunci a gaban kuliya. To amma sai dai a bangaren jam'iyyar PNDS mai mulki na kira da Alkalan da su tabbatar da adalci.

A ranar Alhamis da ta gabata a yayin wata hira da wata kafar yada labaru mai zaman kanta da ke birnin Yamai mai suna Labari ministan na cikin gida Hasumi masa'udu ya yi subul da bakar cewa alkalin da ya nuna cewar baya da hurumin yin shari'ar safarar jarirai na da alaka da wadanda hukumomin ke tuhuma ko zargi da aikata mumunan laifuka. Wadannan kalaman na ministan cikin gida kuma kusa a jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki sun bar baya da kura inda babbar kungiyar alkallai ta kasa ta ce dama ta gaji da yawan yi wa alkallai katsalandan a cikin aiki, alhali kundin tsarin mulkin kasar ya fayyace karfin iko tsakanin bangaren gwamnati da fannin shari'a.

A cikin wani taron manema labarai da alkalan suka yi kungiyar ta yanke hukuncin gurfanar da ministan na cikin gida a gaban shari'a domin yi masa hukumci kan abin da suka kira tozartawa da shafawa alkallai kashin kaji sakamakon tuhumarsu da cewar shari'ar da suka yi akwai lauje cikin nadi.Malam Nouhou Aboubakar mataimakin magatakardan kungiyar ministan ya wuce huruminsa. Gusman Abdulmumuni kusa ne a jam'iyyar ta PNDS Tarayya wanda ya nunar da cewa matakin na alkalan ya saba tsarin mulkin kasar. Wannan dai ba shi ne karon farko ba da alkallan ke fitowa suna nuna rashin jin dadinsu kan tozartar da wasu alkallai ko fannin shari'a.

Sauti da bidiyo akan labarin