Cece-kuce a majalisar dokokin Nijar | Siyasa | DW | 04.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Cece-kuce a majalisar dokokin Nijar

A yayin da majalisar dokokin Nijar ke zama don duba tsarin kasafin kudin badi, batun neman tsige kakaki Hama Amadou na kasa ya na dabo bayan raba gari da ya yi da gwamnati.

Wannan zaman taron majalisar dokoki zai mayar da hankali ne kan tsarin kasafin kudi na shekarar da zata kama, wanda kuma za a yi amfani da su wajen kyautata rayuwar talakawa. Sai dai kuma ya zo ne a daidai lokacin da kakakin majalisar dokoki Malam Hama Amadou ya kaura daga bangaren masu mulki zuwa bangaren masu adawa. A lokacin da aka tambayi Yahouza Sadissou, ministan sadarwa da kuma hulda da hukumin gwamnati ko wannan cece-kucen zai shafi ayyukan tsarin kasafin kudin? Ya kada baki ya ce duk wata dambarwar siyasa ba zata hana 'yan majalisa mai da hankali kan kasafin kudi ba domin aikin kasa ne suka zo yi. saboda haka ne ya yi imani cewar ba za'a samu matsala ba.

Niger Mahamadou Issoufou

Shugaba Mahamadou Issoufou ya raba gari da Hama Amadou

'Yan adawa suka ce talaka bai gani a kasa ba

Malam Kadiri Tidjani dake zaman shugaban gungun 'yan majalisar adawa na ARN ya ce wannan tsarin kasafin kudi da ya wuce bai yi amfani ba don babu wani abu da ya sauya a rayuwar talakawa. Sai dai Assoumana Malam Issa da ke zama dan majalisar PNDS Tarayya ya musanta rashin cin gajiyar talakawa ga ayyukan da gwamnati take yi.

Hama zai ci-gaba da zama kakakin majalisa?

01.06.2013 DW online KARTEN Niger Nianmey

Nijar na cikin kasashen da aka saba cece-kucen siyasa

Game da raba gari da ya yi da bangaren gwamnati kuwa, shugaban majalisar dokoki Hama Adamou ya ce haka da ma demokaradiya ta tanada. Hasali ma dai an sha ganin haka can baya a Nijar. Sai dai ana hasashen cewa bangaren masu mulki za su iya neman tsige shugaban majalisar daga mukaminsa. Dan majalisa Zakari Oumarou wanda ke zama shugaban gungun 'yan majalisar PNDS Tarayya ya ce basu da wannan shirin. Amma ya danganta da yadda shi shugaban majalisa zai tafiyar da aikinsa. Ya ce fatansu wannan abu ya kasance alhairi ga Jamhuriyar Nijar.

Mawallafi: Mahaman Kanta
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

Sauti da bidiyo akan labarin