Cece-kuce a kan nasarar shugaba Mugabe | Labarai | DW | 04.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cece-kuce a kan nasarar shugaba Mugabe

Kasashen duniya na mayar da mabanbantan ra'ayi game da nasarar da Mugabe ya samu a zaben shugaban kasar Zimbabwe

Shugaban kasar Afirka Ta Kudu Jacob zuma ya mika sakon taya murna ga shugaba Robert Mugabe, bisa nasarar da ya samu na lashe zaben shugaban kasar Zimbabwe da ya gudana a ranar Larabar (31.07.13) da ta gabata, a wani abin da ke zama kishiyar matsayin da kasashen yammacin duniya suka dauka na yin watsi da sakamakon zaben, bisa abin da suka ce magudin da aka tafka.

Bayan Allah wadai da gwamnatin Amirka da ma Birtaniya suka yi da zaben, gwamnatin Australiya kuwa kira ta yi ga gudanar da zagaye na biyu na zaben, domin abin da ta ce kura-kuran da aka tafka a zaben farko. Idan ba haka kuwa - a cewar hukumomin na Australiya, ba za su cire takunkumin da suka sanyawa kasar ta Zimbabwe ba.

Masu sanya ido na kasashen Afirka a kan zaben, sun amince da yanda ya gudana, yayin da dan takarar jam'iyyar adawa ta MDC, Morgan Tsvangirai kuwa, ya yi watsi da sakamakon da ya ce satar kuri'u ne kawai, tare da bayyana kudirin kalubalantarsa a gaban kotu.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman