1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Rikici kan dokar hudubar harkokin addinai ya lafa

June 18, 2019

Kura ta lafa a birnin Maradi bayan da hukumomi suka sako Sheik Rayyadu, limamin da aka kama bayan wata huduba da ya yi a game da sabuwar doka kan harkokin addinai.

https://p.dw.com/p/3KdHr
Niger Anti Charlie Hebdo Protest Islam Koran 17.01.2015
Hoto: Reuters/T.Djibo

Mahukuntan birnin Maradi na jamhuriyar Nijar sun sako limamin Juma'a mai suna Sheik Rayyadu ne bayan ya kwashe kusan yini biyu a tsare a sakamakon wata huduba da ya yi kan kudirin doka mai magana game da harkokin addinai a Nijar. Bayan da aka sako shi ya gargadi jama'a da su guji daukan duk wani mataki da zai haifar da hargitsi ko janyo wa kasa asara ta rai ko dukiya.

Rikici ya barke ne bayan da Limamin a yayin huduba ya yi tsokaci kan matakin gwamnati a Jamhuriyar ta Nijar da ta shigar da wani kudirin doka a gaban majalisar dokoki don tsara yadda za a dinga tafiyar da ayyukan addinai, tare da kawo sabon tsari a gina masallatai da sauran wurare ibadun jama'a.

Nan bada jimawa ba, majalisar dokoki ta kasa za ta tafka mahawara a kan wannan kudirin doka mai cike da cece kuce duk kuwa da suka da wannan mataki ke sha, yanzu haka kimanin matasa sama da dari da saba'in da takwas ne ke hannun 'yan sanda sakamakon wannan tarzoma a Nijar.