CDU da SPD za su ƙula ƙawance | Labarai | DW | 17.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

CDU da SPD za su ƙula ƙawance

Jagorar jam'iyyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya ta Jamus CDU Angela Merkel, tare da shugabannin jam'iyyar 'yan demokrat na SPD,za su tattaunawa domin girka sabuwar gwamnati.

An dai kai ga cimma wannan matsayi ne bayan ganawar da aka yi har so uku a jere tsakanin 'yan siyasar ba tare da cimma daidaituwar baki ba.

Angela Merkel wacce ta zo ta farko a zaɓen 'yan majalisun da aka gudanar a cikin watan jiya ta gaza samin rinjaye da zai ba ta damar kafa gwamnati ita ka ɗai. Tun da farko dai jam'iyyar ta CDU ta nemi ta yi ƙawancen da jam'iyyar masu fafutukar kare muhali amma kuma lamarin ya ci tura. Irin wannan ƙawance dai tsakanin SPD da CDU an taɓa yin irinsa a shekarun 1966 zuwa 1969 da kuma shekarun 2005 zuwa 2009 a lokacin wa'adin mulki na farko na Angela Merkel.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasir Awal